Daniyel 4:4-18
4
Ni, Nebukadnezzar, ina zaune a gidana cikin fadata, ina jin daɗi ina bunkasa.
5
Na yi mafarkin da ya ba ni tsoro. A sa’ad da nake kwance a gadona, siffofi da wahayoyi da suka bi ta cikin tunanina sun firgita ni.
6
Don haka na ba da umarni a tattaro dukan masu hikima na Babilon su bayyana a gabana domin su fassara mini mafarkin.
7
Sa’ad da masu sihiri, da masu dabo, da masanan taurari da masu duba suka zo, na faɗa musu mafarkin, amma ba su iya fassarta mini mafarkin ba.
8
A ƙarshe, sai Daniyel ya zo gabana na kuma faɗa masa mafarkin. (Ana ce da shi Belteshazar, wanda aka ba shi sunan allahna kuma ruhun alloli masu tsarki suna a bisansa.)
9
Na ce, “Belteshazar, shugaban masu sihiri, na san ruhun alloli suna a kanka, babu wani asirin da zai fi ƙarfin ganewarka. Ga dai mafarkin da na yi, sai ka fassara mini.
10
Waɗannan su ne wahayin da na gani a lokacin da nake kwance a gadona, na duba, a gabana kuwa ga wani itace a kafe a tsakiyar duniya, yana da tsawo ƙwarai.
11
Itacen ya yi girma ya kuma yi ƙarfi, har tsayinsa ya taɓa sarari sama; ana iya ganinsa a ko’ina a duniya.
12
Ganyayensa suna da kyau, yana da ’ya’ya jingim, abinci kuma domin kowa da kowa. A ƙarƙashinsa namun jeji suke samun wurin hutawa, kuma tsuntsayen sama suna zaune a bisa rassansa; daga cikinsa kowace halitta take cin abinci.
13
“A cikin wahayin da gani sa’ad da nake kwance a kan gadona, Na duba, a gabana kuwa ga wani ɗan saƙo, mai tsarki, yana saukowa daga sama.
14
Sai ya yi kira da babbar murya ya ce, ‘A sare itacen a kuma yayyanka rassansa; a karkaɗe ganyensa a kuma warwatsar da ’ya’yansa. Bari dabbobi su tashi daga ƙarƙashinsa da kuma tsuntsayen da suke a rassansa.
15
Amma a bar kututturen da kuma saiwoyinsa, a daure shi da ƙarfe da kuma tagulla, a bar shi a cikin ƙasa, a cikin ciyayin filaye. “ ‘Bari yă jiƙu da raɓar, bari yă zauna cikin dabbobi tare da tsire-tsiren duniya.
16
Bari a canja tunaninsa irin na mutane a ba shi tunani irin na dabbobi, har sau bakwai su wuce a kansa.
17
“ ‘An sanar da wannan matsayi ne ta bakin ’yan saƙo, masu tsarki ne kuwa suka sanar da hukuncin, domin masu rai su sani Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a bisa kowane mulkin mutane, yakan kuma ba wa duk wanda ya ga dama, yakan sanya talaka yă zama sarki.’
18
“Wannan shi ne mafarkin da ni, Nebukadnezzar, na yi. Yanzu Belteshazar, sai ka faɗa mini abin da yake nufi, domin babu wani a cikin masu hikima a mulkina da ya iya fassara mini shi. Amma za ka iya, domin ruhun alloli masu tsarki yana a bisanka.”
Settings