Skip to content
Ayyukan Manzanni 4:13-22

Ayyukan Manzanni 4:13-22

13
Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu.
14
Amma da yake sun ga mutumin da aka warkar yana tsaye a wurin tare da su, sai suka rasa abin faɗi.
15
Saboda haka suka umarta a fitar da su daga Majalisar, sa’an nan suka yi shawara da juna.
16
Suka ce, “Me za mu yi da waɗannan mutane? Kowa da yake zama a Urushalima ya san sun yi abin banmamaki, kuma ba za mu iya yin mūsu wannan ba.
17
Amma don a hana wannan abu daga ƙara bazuwa cikin mutane, dole mu kwaɓe mutanen nan kada su ƙara yi wa kowa magana cikin wannan suna.”
18
Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu.
19
Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah.
20
Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.”
21
Bayan ƙarin barazana sai suka bar su su tafi. Ba su iya yanke shawara yadda za a hore su ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.
22
Gama mutumin da ya sami warkarwar banmamaki, shekarunsa sun fi arba’in.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options