2 Sama’ila 20:14-22
14
Sheba ya bi ta dukan kabilan Isra’ila zuwa Abel da kuma ta dukan yankin Beriyawa, waɗanda suka taru suka bi shi.
15
Sai dukan rundunonin da suke tare da Yowab suka zo suka yi wa Sheba kwanton ɓauna a Abel-Bet-Ma’aka. Suka tara ƙasa kewaye da jikin katangar birnin daidai da tsayinta. Sa’an nan waɗansu kuma suna ƙoƙarin rushe katangar.
16
Sai wata mata mai hikima ta yi kira daga ciki birnin ta ce, “Ku saurara! Ku saurara! Ku gaya wa Yowab yă zo nan ina so in yi magana da shi.”
17
Ya tafi wurinta, sai ta ce, “Kai ne Yowab?” Ya ce, “Ni ne”. Ta ce, “Ka ji abin da zan ce maka.” Ya ce, “Ina jinki.”
18
Ta ci gaba ta ce, “A dā can, akan ce, ‘Sami amsarka a Abel,’ shi ke nan an gama.
19
Mu ne masu salama da kuma amintattu na Isra’ila. Kana ƙoƙari ka hallaka birnin da yake uwa a Isra’ila. Don me kake so ka hallakar da gādon Ubangiji?”
20
Yowab ya ce, “Allah yă sawwaƙe! Allah yă sawwaƙe in hallaka, ko in lalace gādon Ubangiji.
21
Ba haka ba ne batun. Wani mai suna Sheba ɗan Bikri ne, daga ƙasar tudun Efraim, ya tayar wa sarki, yana gāba da Dawuda. Ki ba mu wannan mutum, zan kuwa janye daga birnin.” Matar ta ce wa Yowab, “Za a jefa maka kansa daga katanga.”
22
Sa’an nan matar ta tafi wurin dukan mutane da shawararta mai hikima, sai suka datse kan Sheba ɗan Bikri suka jefa wa Yowab. Saboda haka sai ya busa ƙaho, mutanensa kuwa suka watse daga birnin, kowa ya koma gidansa. Yowab kuma ya koma wurin sarki a Urushalima.
Settings