2 Tarihi 5:2-8
2
Sa’an nan Solomon ya tattara zuwa Urushalima dattawan Isra’ila, dukan kawunan kabilu da manyan iyalan Isra’ilawa, don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda.
3
Dukan mutanen Isra’ila kuwa suka tattaru gaba ɗaya suka zo wurin sarki a lokacin biki a wata na bakwai.
4
Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka iso, Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin,
5
suka haura da akwatin alkawarin da kuma Tentin Sujada da dukan kayayyaki masu tsarkin da yake cikinta. Firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, suka ɗauke su;
6
Sarki Solomon kuwa da taron Isra’ila gaba ɗaya da suka taru kewaye da shi suna a gaban akwatin alkawarin, suna miƙa tumaki da shanu masu yawa da suka wuce ƙirge ko lissafi.
7
Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurinsa a ciki cikin wuri mai tsarki na haikali, Wuri Mafi Tsarki, suka sa shi ƙarƙashin fikafikan kerubobin.
8
Kerubobin suka buɗe fikafikansu a bisa wurin akwatin alkawari suka kuma rufe akwatin alkawarin da sandunan ɗaukonsa.
Settings