Skip to content
2 Tarihi 4:19-22

2 Tarihi 4:19-22

19
Solomon ya kuma yi dukan kayayyakin da suke a cikin haikalin Allah. Bagaden zinariya; teburin da ake ajiye burodin Kasancewa;
20
wurin ajiye fitila na zinariya zalla tare da fitilunsu, don ƙonawa a gaban wuri mai tsarki na ciki kamar yadda aka tsara;
21
aikin zānen furannin zinariya da fitilu da abin ɗiban wuta (an yi su da zinariya zalla);
22
arautaki; kwanonin yayyafawa, kwanoni da hantsuka; da kuma ƙofofin zinariya na haikali, ƙofofi na ciki zuwa Wuri Mafi Tsarki da kuma ƙofofin babban zaure.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options