2 Tarihi 4:11-18
11
Ya kuma yi tukwane da manyan cokula da kwanonin yayyafawa. Ta haka Huram ya gama aikin da ya yi wa Sarki Solomon a cikin haikalin Allah.
12
Ginshiƙai biyu; kwanoni biyu masu siffar kwartaniya a bisa ginshiƙai; jeri biyu na tuƙaƙƙen adon kwanonin yayyafawa masu siffar kwartaniya a bisa ginshiƙai;
13
rumman ɗari huɗu don jeri biyu na tuƙaƙƙe (layi biyu na rumman don kowane tuƙaƙƙe, mai adon kwano mai siffar kwartaniya a bisan ginshiƙai);
14
dakalai da darunansu;
15
ya yi kwanon da ya kira Teku, da bijimai goma sha biyu a ƙarƙashinsa;
16
tukwane, manyan cokula, cokula masu yatsu don nama da dukan kayayyakin da suka shafi wannan. Dukan kayayyakin da Huram-Abi ya yi domin Sarki Solomon saboda haikalin Ubangiji an yi su da gogaggen tagulla ne.
17
Sarki ya sa aka yi zubinsu a katakon yin tubali a filin Urdun tsakanin Sukkot da Zereda.
18
Dukan waɗannan abubuwa da Solomon ya yi suna da tsada ƙwarai har suka kai nauyin tagullar da ya fi misali.
Settings