2 Tarihi 36:1-8
1
Sai mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoyahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki a Urushalima yă gāji mahaifinsa.
2
Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku.
3
Sarkin Masar ya tumɓuke shi a Urushalima, ya tilasta Yahuda su biya haraji talenti ɗari na azurfa da kuma talentin zinariya.
4
Sarkin Masar ya naɗa Eliyakim, ɗan’uwan Yehoyahaz, sarki a bisa Yahuda da kuma Urushalima, ya kuma canja sunan Eliyakim zuwa Yehohiyakim. Amma Neko ya ɗauki Yehoyahaz ɗan’uwan Eliyakim ya kai Masar.
5
Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa.
6
Nebukadnezzar sarkin Babilon ya hauro ya kara da shi. Ya kama shi, ya daure da sarƙoƙin tagulla, ya kuma kai shi Babilon.
7
Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kuma kwaso kayayyaki daga haikalin Ubangiji ya sa su a haikalinsa a can.
8
Sauran ayyukan mulkin Yehohiyakim, ayyukan banƙyamar da ya aikata da dukan abubuwan da aka same shi da su, suna a rubuce cikin littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda. Sai Yehohiyacin ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings