Skip to content
2 Tarihi 28:5-15

2 Tarihi 28:5-15

5
Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya miƙa shi ga sarkin Aram. Arameyawa suka ci shi a yaƙi, suka kuma kwashe mutanensa da yawa a matsayin ’yan kurkuku, suka kawo Damaskus. Ya kuma ba da shi ga sarkin Isra’ila, wanda ya jijji masa a yaƙi.
6
A rana ɗaya Feka ɗan Remaliya ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu ashirin a Yahuda, domin Yahuda sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu.
7
Zikri, wani jarumin Efraim, ya kashe Ma’asehiya ɗan sarki, Azrikam hafsa mai lura da fada, da kuma Elkana, mataimakin sarki.
8
Isra’ilawa suka kame kamammu daga ’yan’uwansu mata, ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata dubu ɗari biyu. Suka kuma kwashe ganima mai yawan gaske, waɗanda suka kwasa zuwa Samariya.
9
Amma wani annabin Ubangiji mai suna Oded yana a can, sai ya fito don yă sadu da mayaƙa sa’ad da suke komowa zuwa Samariya. Ya ce musu, “Domin Ubangiji Allah na kakanninku yana fushi da Yahuda, ya ba da su cikin hannunku. Sai kuka kashe su cikin fushin da ya kai sama.
10
Yanzu kuma kuna niyya ku mai da maza da matan Yahuda da Urushalima bayinku. Amma ku ɗin ba ku da laifin zunubi ga Ubangiji Allahnku ne?
11
To, ku saurare ni! Ku mai da ’yan’uwanku da kuka kama a matsayin ’yan kurkuku, gama fushin Ubangiji yana a kanku.”
12
Sai waɗansu shugabanni a Efraim, Azariya ɗan Yehohanan, Berekiya ɗan Meshillemot, Hezekiya ɗan Shallum da Amasa ɗan Hadlai, suka tasar wa waɗanda suke isowa daga yaƙi.
13
Suka ce, “Dole ku kawo waɗannan ’yan kurkukun a nan, ko kuwa za ku yi laifi a gaban Ubangiji. Kuna niyya ku ƙara ga zunubinmu da kuma laifinmu? Gama laifinmu ya riga ya yi yawa, kuma fushinsa mai tsanani yana a kan Isra’ila.”
14
Saboda haka sojoji suka ba da ’yan kurkukun da ganima a gaban hafsoshi da dukan taron.
15
Sai mutanen da aka kira sunansu suka tashi, suka ɗauki kamammun, da ganimar, suka sa wa dukan waɗanda suke tsirara sutura. Suka sa musu sutura, suka ba su takalma, suka ba su abinci da abin sha, suka shafa musu mai. Suka hawar da dukan raunana a kan jakuna, suka kai su wurin ’yan’uwansu a Yeriko, wato, Birnin Itatuwan Dabino, sa’an nan suka koma Samariya.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options