2 Tarihi 26:6-15
6
Ya yi yaƙi da Filistiyawa ya kuma rushe katangar Gat, Yabne da kuma Ashdod. Sa’an nan ya sāke gina garuruwa kusa da Ashdod da sauran wurare a cikin Filistiyawa.
7
Allah ya taimake shi a kan Filistiyawa da kuma a kan Larabawa waɗanda suke zama a Gur-Ba’al da kuma a kan Meyunawa.
8
Ammonawa suka kawo haraji wa Uzziya, sunan da ya yi kuwa ya bazu har iyakar Masar, domin ya zama mai iko sosai.
9
Uzziya ya gina hasumiyoyi a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, a Ƙofar Kwari da kuma a kusurwar katanga, ya kuma yi musu katanga.
10
Ya gina hasumiyoyi a hamada ya kuma haƙa rijiyoyi masu yawa, gama yana da dabbobi masu yawa a gindin duwatsu da kuma a kwari. Yana da mutane masu yin masa aiki a gonakinsa da gonakin inabinsa a tuddai da kuma a ƙasashe masu dausayi, gama yana son noma.
11
Uzziya ya kasance da gogaggun mayaƙa, a shirye su fito ɓangarori-ɓangarori bisa ga yawansu yadda Yehiyel magatakarda, da Ma’asehiya jarumi, suka karkasa su bisa ga umarnin Hananiya, ɗaya daga cikin fadawa.
12
Yawan shugabannin iyali a bisa jarumawa sun kai 2,600.
13
A ƙarƙashin shugabancinsu akwai mayaƙa 307,500 horarru don yaƙi, mayaƙa masu ƙarfi don su taimaki sarki a kan abokan gābansa.
14
Uzziya ya tanada garkuwoyi, māsu, hulunan kwano, kayan sulke, baka da majajjawa don mayaƙan gaba ɗaya.
15
A Urushalima ya yi na’urori da gwanaye suka sarrafa don amfani a hasumiyoyi da kuma a kusurwar kāriya don harbin kibiyoyi da jefan manyan duwatsu. Sunansa ya bazu ko’ina, gama ya sami taimako sosai har ya zama mai iko.
Settings