2 Tarihi 10:12-19
12
Bayan kwana uku sai Yerobowam da dukan mutane suka dawo wurin Rehobowam, yadda sarki ya ce, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.”
13
Sarki ya amsa musu da kakkausar murya. Ya ƙi shawarar dattawan,
14
ya kuma bi shawarar matasan ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; zan ma sa mafi nauyi. Mahaifina ya bulale ku da bulala; zan bulale ku da kunamai.”
15
Saboda haka sarki bai saurari mutane ba, gama wannan juyin al’amura daga Allah ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi ga Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya mutumin Shilo.
16
Sa’ad da Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, suka ce, “Wanda rabo muke da shi a wurin Dawuda, wanda sashe muke da shi daga ɗan Yesse? Kowa yă koma tentinsa, ya Isra’ila! Ka lura da gidanka, ya Dawuda!” Saboda haka dukan Isra’ilawa suka tafi gida.
17
Amma game da Isra’ilawan da suke zama a garuruwan Yahuda kuwa, Rehobowam ya ci gaba da yin mulki a bisansu.
18
Sarki Rehobowam ya aiki Hadoram wanda yake lura da aikin dole, amma Isra’ilawa suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sarki Rehobowam kuwa ya gaggauta ya shiga keken yaƙinsa ya gudu zuwa Urushalima.
19
Ta haka Isra’ila ya kasance cikin tawaye a kan gidan Dawuda har yă zuwa wannan rana.
Settings