Skip to content
1 Bitrus 3:8-22

1 Bitrus 3:8-22

8
A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar ’yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u.
9
Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka.
10
Gama, “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa, yă kuma ga kwanaki masu kyau dole yă ƙame harshensa daga mugunta leɓunansa kuma daga maganar yaudara.
11
Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta; dole yă nemi salama yă kuma bi ta.
12
Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu, amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”
13
Wa zai yi muku lahani in kun himmantu ga yin nagarta?
14
Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.”
15
Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi,
16
tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi.
17
Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta.
18
Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu,
19
ta wurin wanda kuma ya tafi ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku wa’azi
20
waɗanda dā ba su yi biyayya ba sa’ad da Allah ya jira da haƙuri a kwanaki Nuhu yayinda ake sassaƙa jirgi. A cikinsa mutane kima ne kawai, su takwas, aka kuɓutar ta ruwa,
21
ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma, ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,
22
wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah, mala’iku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options