Skip to content
1 Sarakuna 8:12-61

1 Sarakuna 8:12-61

12
Sai Solomon ya ce, “Ubangiji ya ce zai zauna a gizagizai masu duhu;
13
ga shi na gina haikali mai daraja dominka, inda za ka zauna har abada.”
14
Yayinda dukan taron Isra’ila suke tsattsaye a can, sai sarki ya juya ya albarkace su.
15
Sa’an nan ya ce, “Ku yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda da hannunsa ya cika abin da ya yi alkawari da bakinsa ga mahaifina Dawuda. Gama ya ce,
16
‘Tun ran da na fitar da mutanena Isra’ila daga Masar, ban zaɓi wani birni a cikin wata kabilar Isra’ila a gina haikali domin Sunana yă kasance a can ba, amma na zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’
17
“Mahaifina Dawuda ya yi niyya a cikin zuciyarsa yă gina haikali saboda Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.
18
Amma Ubangiji ya ce wa mahaifina Dawuda, ‘Saboda yana a zuciyarka ka gina haikali domin Sunana, ka yi daidai da ka yi niyyar wannan a zuciyarka.
19
Duk da haka, ba kai ba ne za ka gina haikali, amma ɗanka, wanda yake namanka da jininka, shi ne wanda zai gina haikali domin Sunana.’
20
“Ubangiji ya kiyaye alkawarin da ya yi. Na gāje Dawuda mahaifina, yanzu kuma ga shi na zauna a kujerar sarautar Isra’ila, kamar dai yadda Ubangiji ya yi alkawari, na kuma gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.
21
Na tanada wuri saboda akwatin alkawari, akwatin da ya ƙunshi alkawarin da Ubangiji ya yi da kakanninmu sa’ad da ya fitar da su daga Masar.”
22
Sai Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji, a gaban dukan taron Isra’ila, ya ɗaga hannuwansa sama,
23
ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama can bisa, ko a ƙasa can ƙarƙashi, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna ga bayinka waɗanda suke cin gaba a hanyarka da dukan zuciyarsu.
24
Ka kiyaye alkawarinka da ka yi wa bawanka Dawuda mahaifina. Da bakinka ka yi alkawari, da hannunka kuma ka cika shi, yadda yake a yau.
25
“Yanzu, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari ka cika wa bawanka Dawuda mahaifina alkawaran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza sun yi hankali cikin dukan abubuwan da suke yi, don su yi tafiya a gabana kamar yadda ka yi.’
26
Yanzu fa, ya Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi wa bawanka Dawuda mahaifina tă cika.
27
“Amma anya, Allah, za ka zauna a duniya? Sammai, har ma da saman sammai ba za tă iya riƙe ka ba, balle wannan haikalin da na gina!
28
Duk da haka ka ji addu’ar bawanka da kuma roƙonsa don jinƙai, ya Ubangiji Allahna. Ka ji kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka a wannan rana.
29
Bari idanunka su buɗe, su fuskanci wannan haikali dare da rana, wannan wurin da ka ce, ‘Sunana zai kasance a can,’ saboda ka ji addu’ar bawanka in yana fuskantar wannan wuri.
30
Ka ji roƙon bawanka da kuma na mutanenka Isra’ila sa’ad da suka yi addu’a, suka fuskanci wannan wuri. Ka ji daga sama, mazauninka, kuma sa’ad da ka ji, ka gafarta.
31
“Sa’ad da mutum ya yi abin da ba daidai ba ga maƙwabcinsa, an kuma bukace shi yă yi rantsuwa, sai ya zo ya rantse a gaban bagade a cikin haikalin nan,
32
sai ka ji daga sama, ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, ka hukunta mai laifi, ka mai da laifinsa a kansa, mai gaskiya kuma ka nuna shi marar laifi ne bisa ga gaskiyarsa.
33
“Sa’ad da abokan gāba suka ci mutanenka Isra’ila a yaƙi saboda sun yi maka zunubi, sa’ad da kuma suka dawo gare ka don su furta sunanka, suna addu’a suna roƙo gare ka a wannan haikali,
34
ka ji daga sama, ka gafarta zunubin mutanenka, ka kuma dawo da su ƙasar da ka ba wa kakanninsu.
35
“Sa’ad da sammai sun kulle, babu kuma ruwan sama domin mutane sun yi maka zunubi, sa’ad da suka yi addu’a suna fuskantar wannan wuri, suka kuma furta sunanka, suka juye daga zunubinsu domin ka hore su,
36
ka ji daga sama, ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace ta rayuwa, ka kuma aika da ruwan sama a ƙasar da ka ba wa mutanenka gādo.
37
“Sa’ad da yunwa ko annoba ta fāɗo a ƙasar, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, ko kuwa abokan gāba sun yi musu kwanto, a wani daga cikin biranensu, duk wata cuta, ko ciwon da ya zo,
38
in suka yi addu’a ko roƙo ta wurin wani daga cikin mutanenka Isra’ila, kowa ya san wahalar zuciyarsa, ya kuma buɗe hannuwansa yana fuskantar wannan haikali,
39
sai ka ji daga sama, mazauninka. Ka gafarta, ka kuma yi wani abu. Ka yi da kowane mutum bisa ga dukan abin da ya yi, tun da yake ka san zuciyarsa (gama kai kaɗai ka san zukatan dukan mutane),
40
saboda su ji tsoronka a kowane lokacin da suke zaune a ƙasar da ka ba wa kakanninmu.
41
“Game da baƙo kuwa wanda shi ba na mutanenka Isra’ila ba, amma ya zo daga ƙasa mai nisa saboda sunanka,
42
gama mutane za su ji game da girman sunanka, da ƙarfin hannunka, da kuma hannunka mai iko, sa’ad da ya zo, ya yi addu’a yana fuskantar wannan haikali,
43
ka ji daga sama, mazauninka, ka kuma yi dukan abin da baƙon ya tambaye ka, saboda dukan mutanen duniya su san sunanka, su kuma ji tsoronka, kamar yadda mutanenka Isra’ila suke yi, bari kuma su san cewa wannan gidan da na gina, ya amsa Sunanka.
44
“Sa’ad da mutanenka suka tafi yaƙi da abokan gābansu, a duk inda ka aike su, sa’ad da kuma suka yi addu’a ga Ubangiji suna fuskantar birnin da ka zaɓa, da kuma haikalin da na gina domin Sunanka,
45
ka ji addu’arsu da roƙonsu daga sama, ka kuma biya musu bukatansu.
46
“Sa’ad da suka yi maka zunubi, gama babu wanda ba ya zunubi, ka kuwa yi fushi da su, ka kuma ba da su ga abokin gāba, wanda ya kwashe su kamammu zuwa ƙasarsa, nesa ko kusa;
47
in suka canja zuciyarsu a ƙasar da aka riƙe su kamammu, suka tuba, suka kuma roƙe ka a ƙasar waɗanda suka ci su da yaƙi, suka ce, ‘Mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba, mun yi mugunta’;
48
in sun juye gare ka da dukan zuciyarsu, da dukan ransu a ƙasar abokan gābansu waɗanda suka kwashe kamammu, suka yi addu’a gare ka, suka fuskanci wajen ƙasar da ka ba wa kakanninsu, waje birnin da ka zaɓa, da kuma haikalin da na gina domin Sunanka;
49
sai ka ji daga sama, mazauninka, ka ji addu’a da roƙonsu, ka kuma biya musu bukatansu.
50
Ka gafarta wa mutanenka, waɗanda suka yi maka zunubi; ka gafarta dukan laifofin da suka yi maka, ka kuma sa waɗanda suka ci su a yaƙi su ji tausayinsu.
51
Gama su mutanenka ne, abin gādonka, waɗanda ka fitar daga Masar, daga tanderu mai narken ƙarfe.
52
“Bari idanunka su buɗe ga roƙon bawanka, ga roƙon mutanenka Isra’ila, bari kuma ka saurare su sa’ad da suka yi kuka gare ka.
53
Gama ka ware su daga dukan al’umman duniya su zama abin gādonka, kamar yadda aka furta ta wurin bawanka Musa sa’ad da kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka ka fitar da kakanninmu daga Masar.”
54
Da Solomon ya gama dukan waɗannan addu’o’i da roƙe-roƙe ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda ya durƙusa da hannuwansa a buɗe waje sama.
55
Ya tashi ya kuma albarkaci dukan taron Isra’ila da babbar murya, yana cewa,
56
“Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya ba wa mutanensa hutu kamar dai yadda ya yi alkawari. Babu magana guda da ta kāsa cika cikin dukan alkawaransa masu kyau da ya yi ta wurin bawansa Musa.
57
Bari Ubangiji Allah yă kasance tare da mu kamar yadda ya kasance da kakanninmu; kada yă taɓa rabu da mu, ko yă yashe mu.
58
Bari yă juye zukatanmu gare shi, don mu yi tafiya a cikin dukan hanyoyinsa, mu kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa, da kuma farillan da ya ba wa kakanninmu.
59
Bari kuma waɗannan kalmomina, waɗanda na yi addu’a a gaban Ubangiji, su yi kusa da Ubangiji Allahnmu, dare da rana, don yă biya bukatan bawansa da na mutanensa Isra’ila, bisa ga bukatan kowa,
60
saboda dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji, shi ne Allah, babu kuma wani.
61
Amma dole ku miƙa zukatanku ga Ubangiji Allahnmu, don ku rayu, ta wurin bin ƙa’idodinsa, ku kuma yi biyayya da umarnansa, kamar yadda kuke yi a wannan lokaci.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options