1 Sarakuna 15:9-24
9
A shekara ta ashirin ta Yerobowam sarkin Isra’ila, Asa ya zama sarkin Yahuda,
10
ya yi mulki a Urushalima shekara arba’in da ɗaya. Sunan mahaifiya mahaifiyarsa, Ma’aka ne ’yar Abisalom.
11
Asa ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi.
12
Ya kori dukan maza karuwai na masujadai daga ƙasar, ya kuma yi waje da dukan gumakan da mahaifinsa ya yi.
13
Ya tuɓe mahaifiya mahaifiyarsa Ma’aka daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, gama ta gina ƙazantaccen ginshiƙin Ashera. Asa ya yanke ginshiƙin, ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron.
14
Ko da yake bai cire masujadai da suke kan tuddai ba, zuciyar Asa ta kasance da aminci ɗungum ga Ubangiji dukan kwanakinsa.
15
Ya kawo azurfa da zinariya da kayayyakin da shi da mahaifinsa suka keɓe a haikalin Ubangiji.
16
Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu.
17
Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura, ya yi yaƙi da Yahuda, ya kuma gina Rama don yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa, sarkin Yahuda.
18
Sai Asa ya ɗauki dukan azurfa da kuma zinariyar da suka rage a ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma nasa fadan, ya ba da su ga wani shugabansa, ya kuma aika da su zuwa ga Ben-Hadad ɗan Tabrimmon, ɗan Heziyon, sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus.
19
Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakanina da kai, kamar yadda ta kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, ina aika maka kyautai na azurfa da na zinariya. Yanzu fa sai ka janye yarjejjeniyarka da Ba’asha sarkin Isra’ila, don yă janye daga gare ni.”
20
Ben-Hadad ya yarda da maganar Sarki Asa, ya kuma aika shugabannin sojojin mayaƙansa ya yi yaƙi da garuruwan Isra’ila. Ya kame Iyon, Dan, Abel-Bet-Ma’aka da dukan Kinneret, haɗe da Naftali.
21
Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina ginin Rama, ya janye zuwa Tirza.
22
Sai Sarki Asa ya ba da umarni ga dukan Yahuda, kuma babu wanda aka ware, kowa yă taimaka a kwashe duwatsu da katakan da Ba’asha yake amfani da su daga Rama. Da duwatsu da katakan ne Sarki Asa ya gina Geba a Benyamin da kuma Mizfa.
23
Game da sauran ayyukan mulkin Asa, dukan nasarorinsa, dukan abin da ya yi, da kuma biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. A tsufansa, sai ƙafafunsa suka kamu da cuta.
24
Sai Asa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a birnin kakansa Dawuda. Sai Yehoshafat ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
Settings