1 Sarakuna 15:1-8
1
A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yerobowam ɗan Nebat, Abiyam ya zama sarkin Yahuda,
2
ya kuma yi mulki a Urushalima shekara uku. Sunan mahaifiyarsa Ma’aka ne, ’yar Abisalom.
3
Shi ma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Zuciyarsa ba tă bi Ubangiji Allahnsa, kamar yadda zuciyar Dawuda kakansa ta yi ba.
4
Duk da haka, saboda Dawuda Ubangiji Allahnsa ya ba shi fitila a Urushalima ta wurin ta da wani da ya gāje shi, ta wurinsa kuma Urushalima ta yi ƙarfi.
5
Gama Dawuda ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, bai kuma fasa kiyaye wani daga umarnan Ubangiji ba dukan kwanakinsa, sai dai a batun Uriya mutumin Hitti.
6
Aka yi yaƙi tsakanin Rehobowam da Yerobowam a duk kwanakin Abiya.
7
Game da sauran ayyukan mulkin Abiyam kuwa, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. Aka yi yaƙi tsakanin Abiyam da Yerobowam.
8
Sai Abiyam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.
Settings