1 Tarihi 6:54-81
54
Waɗannan su ne wuraren zamansu da aka ba su rabo su zama yankunansu (aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga gidan Kohat, domin rabo na fari nasu ne):
55
Aka ba su Hebron a Yahuda tare da wuraren kiwon da suke kewayenta.
56
Amma filaye da ƙauyukan da suke kewayen birnin aka ba wa Kaleb ɗan Yefunne.
57
Saboda haka aka ba wa zuriyar Haruna Hebron (birnin mafaka), da Libna, Yattir Eshtemowa,
58
Hilen, Debir,
59
Ashan, Yutta da Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu.
60
Daga kabilar Benyamin kuma aka ba su Gibeyon, Geba, Alemet da Anatot, tare da wuraren kiwonsu. Waɗannan garuruwa waɗanda aka raba a tsakanin mutanen gidan Kohat, goma sha uku ne duka.
61
Aka ba sauran zuriyar Kohat rabon garuruwa goma daga gidajen rabin kabilar Manasse.
62
Aka ba zuriyar Gershom, gida-gida, rabon garuruwa goma sha uku daga kabilan Issakar, Asher da Naftali, da kuma daga sashen rabi kabilar Manasse da yake a Bashan.
63
Aka ba zuriyar Merari, gida-gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.
64
Saboda haka Isra’ilawa suka ba Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwonsu.
65
Daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin suka ba su rabon sunayen garuruwan da aka ambata.
66
Aka ba wa waɗansu na mutanen gidan Kohat yankin garuruwansu daga kabilar Efraim.
67
A ƙasar tudun Efraim aka ba su Shekem (birnin mafaka), da Gezer,
68
Yokmeyam, Bet-Horon,
69
Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu.
70
Daga rabin kabilar Manasse kuwa, Isra’ilawa suka ba da Aner da Bileyam, tare da wuraren kiwonsu, ga sauran gidajen mutanen Kohat.
71
Mutanen Gershom suka sami waɗannan. Daga gidan rabin kabilar Manasse, sun sami Golan a Bashan da kuma Ashtarot, tare da wuraren kiwonsu;
72
daga kabilar Issakar suka sami Kedesh, Daberat,
73
Ramot da Anem, tare da wuraren kiwonsu;
74
daga kabilar Asher suka sami Mashal, Abdon,
75
Hukok da Rehob, tare da wuraren kiwonsu;
76
daga kabilar Naftali kuwa suka sami Kedesh a Galili, Hammon da Kiriyatayim, tare da wuraren kiwonsu.
77
Mutanen Merari (sauran Lawiyawan) suka sami waɗannan. Daga kabilar Zebulun suka sami Yokneyam, Karta, Rimmon da Tabor, tare da wuraren kiwonsu;
78
daga kabilar Ruben a hayin Urdun a gabashi Yeriko suka sami Bezer a hamada, Yahza,
79
Kedemot da Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu;
80
daga kabilar Gad kuwa suka sami Ramot a Gileyad, Mahanayim,
81
Heshbon da Yazer, tare da wuraren kiwonsu.
Settings