1 Tarihi 6:49-53
49
Amma Haruna da zuriyarsa su ne waɗanda suke miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa da kuma a kan bagaden turare haɗe da dukan abin da ake yi a Wuri Mafi Tsarki, suna yin kafara domin Isra’ila, bisa ga dukan abin da Musa bawan Allah ya umarta.
50
Waɗannan su ne zuriyar Haruna, Eleyazar, Finehas, Abishuwa,
51
Bukki, Uzzi, Zerahiya,
52
Merahiyot, Amariya, Ahitub,
53
Zadok da Ahimawaz.
Settings