Skip to content
1 Tarihi 21:5-17

1 Tarihi 21:5-17

5
Yowab ya ba labarin yawan mayaƙan wa Dawuda. A cikin Isra’ila akwai mutum miliyon da dubu ɗari ɗaya waɗanda za su iya riƙe takobi, haɗe da dubu ɗari huɗu da saba’in a Yahuda.
6
Amma Yowab bai haɗa da mutanen Lawi da na Benyamin a ƙidayar ba, domin bai ji daɗin umarnin sarki ba.
7
Wannan umarnin mugu ne a gaban Allah; saboda haka ya hukunta Isra’ila.
8
Sai Dawuda ya ce wa Allah, “Na yi zunubi ƙwarai ta wurin yin wannan. Yanzu, na roƙe ka, ka ɗauke laifin bawanka. Na yi wauta sosai.”
9
Sai Ubangiji ya ce wa Gad, mai duba na Dawuda,
10
“Tafi ka faɗa wa Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ina ba ka abubuwa uku. Ka zaɓi ɗaya daga cikinsu don in aikata a kanka.’ ”
11
Saboda haka Gad ya tafi wurin Dawuda ya ce masa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ka yi zaɓi,
12
shekara uku na yunwa, wata uku na shan ɗibga a gaban abokan gābanka, sa’ad da za su bi suna kakkashe ku, ko kuwa kwana uku na takobin Ubangiji, ranakun annoba a cikin ƙasar, mala’ikan Ubangiji zai hallaka kowane sashe na Isra’ila.’ Yanzu sai ka yanke shawara yadda zan amsa wa wanda ya aiko ni.”
13
Dawuda ya ce wa Gad, “Na shiga uku. Bari in fāɗa a hannuwan Ubangiji, gama jinƙansa yana da girma sosai; amma kada ka bari in fāɗa a hannuwan mutane.”
14
Sai Ubangiji ya aiko da annoba a kan Isra’ila, mutane duba saba’in na Isra’ila suka mutu.
15
Allah kuwa ya aiki mala’ika yă hallaka Urushalima. Amma yayinda mala’ikan yana gab da yin haka, sai Ubangiji ya gani ya kuma yi nadama saboda masifar, sai ya ce wa mala’ikan wanda yake hallaka mutane, “Ya isa! Janye hannunka.” Mala’ikan Ubangiji kuwa yana tsaye a masussukar Ornan mutumin Yebus.
16
Sai Dawuda ya ɗaga ido ya ga mala’ikan Ubangiji tsaye tsakanin sama da duniya, da takobi a zāre a hannunsa ya miƙa a kan Urushalima. Sai Dawuda da dattawa, saye da rigunan makoki suka fāɗi rubda jiki.
17
Dawuda ya ce wa Allah, “Ba ni ba ne na umarta a ƙidaya mayaƙan? Ni ne wanda ya yi zunubin da kuma abin da ba daidai ba. Waɗannan dai tumaki ne. Me suka yi? Ya Ubangiji Allahna, bari hannunka ya fāɗi a kaina da kuma iyalina, amma kada ka bar wannan annoba ya kasance a kan mutanenka.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options