Skip to content
1 Tarihi 2:42-55

1 Tarihi 2:42-55

42
’Ya’yan Kaleb maza, ɗan’uwan Yerameyel su ne, Mesha ɗan farinsa, wanda shi ne mahaifin Zif, da ɗansa Maresha, wanda shi ne mahaifin Hebron.
43
’Ya’yan Hebron maza su ne, Kora, Taffuwa, Rekem da Shema.
44
Shema shi ne mahaifin Raham, Raham kuma shi ne mahaifin Yorkeyam. Rekem shi ne mahaifin Shammai.
45
Ɗan Shammai shi ne Mawon, Mawon kuma shi ne mahaifin Bet-Zur.
46
Efa ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Haran, Moza da Gazez. Haran shi ne mahaifin Gazez.
47
’Ya’yan Yadai maza su ne, Regem, Yotam, Geshan, Felet, Efa da Sha’af.
48
Ma’aka ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Sheber da Tirhana.
49
Ta kuma haifi Sha’af mahaifin Madmanna da kuma Shewa, mahaifin Makbena da Gibeya. ’Yar Kaleb ita ce Aksa.
50
Waɗannan su ne zuriyar Kaleb. ’Ya’yan Hur maza, ɗan farin Efrata su ne, Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim,
51
Salma mahaifin Betlehem, da kuma Haref mahaifin Bet-Gader.
52
Zuriyar Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim su ne, Harowe, rabin Manahatiyawa,
53
kuma gidan Kiriyat Yeyarim su ne, Itrayawa, Futiyawa, Shumatiyawa da Mishratiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito.
54
Zuriyar Salma su ne, Betlehem, Netofawa, Atrot Bet Yowab, rabin Manahatiyawa, Zoriyawa,
55
kuma gidan marubuta waɗanda suke zama a Yabez su ne, Tiratiyawa, Shimeyatiyawa da Sukatiyawa. Waɗannan su ne Keniyawa waɗanda suka zo daga Hammat, mahaifin gidan Rekab.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options