1 Tarihi 2:25-41
25
’Ya’yan Yerameyel maza, ɗan farin Hezron su ne, Ram shi ne ɗan fari, sai Buna, Oren, Ozem da Ahiya.
26
Yerameyel yana da wata mata, wadda sunanta Atara; ita ce mahaifiyar Onam.
27
’Ya’yan Ram maza ɗan farin Yerameyel su ne, Ma’az, Yamin da Eker.
28
’Ya’yan Onam maza su ne, Shammai da Yada. ’Ya’yan Shammai maza su ne, Nadab da Abishur.
29
Sunan matar Abishur ita ce Abihayil, wadda ta haifa masa Aban da Molid.
30
’Ya’yan Nadab maza su ne, Seled da Affayim. Seled ya mutu babu yara.
31
Ɗan Affayim shi ne, Ishi, wanda shi ne mahaifin Sheshan. Sheshan shi ne mahaifin Alai.
32
’Ya’yan Yada maza, ɗan’uwan Shammai su ne, Yeter da Yonatan. Yeter ya mutu babu yara.
33
’Ya’yan Yonatan maza su ne, Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yerameyel.
34
Sheshan ba shi da ’ya’ya maza, sai ’ya’ya mata kawai. Yana da bawa mutumin Masar mai suna Yarha.
35
Sheshan ya ba da ’yarsa aure ga bawansa Yarha, ta kuwa haifa masa Attai.
36
Attai shi ne mahaifin Natan, Natan shi ne mahaifin Zabad,
37
Zabad shi ne mahaifin Eflal, Eflal shi ne mahaifin Obed,
38
Obed shi ne mahaifin Yehu, Yehu shi ne mahaifin Azariya,
39
Azariya shi ne mahaifin Helez, Helez shi ne mahaifin Eleyasa,
40
Eleyasa shi ne mahaifin Sismai, Sismai shi ne mahaifin Shallum
41
Shallum shi ne mahaifin Yekamiya, Yekamiya kuma shi ne mahaifin Elishama.
Settings