1 Tarihi 2:18-24
18
Kaleb ɗan Hezron ya haifi yara ta wurin matarsa Azuba (da kuma ta wurin Yeriyot). Waɗannan su ne ’ya’yan Azuba maza. Yesher, Shobab da Ardon.
19
Da Azuba ta mutu, Kaleb ya auri Efrat, wadda ta haifa masa Hur.
20
Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuma shi ne mahaifin Bezalel.
21
Daga baya, Hezron ya kwana da ’yar Makir mahaifin Gileyad (ya aure ta sa’ad da take da shekara sittin), ta haifa masa Segub.
22
Segub shi ne mahaifin Yayir, wanda ya yi mulkin garuruwa uku a Gileyad.
23
(Amma Geshur da Aram suka ƙwace Hawwot Yayir da kuma Kenat tare da ƙauyukan kewayenta, garuruwa sittin.) Dukan waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad.
24
Bayan Hezron ya mutu a Kaleb Efrata, sai Abiya matar Hezron ta haifa masa Asshur mahaifin Tekowa.
Settings