1 Tarihi 2:9-17
9
’Ya’ya maza da aka haifa wa Hezron su ne, Yerameyel, Ram da Kaleb.
10
Ram shi ne mahaifin Amminadab, Amminadab kuwa shi ne mahaifin Nashon, shugaban mutanen Yahuda.
11
Nashon shi ne mahaifin Salma, Salma shi ne mahaifin Bowaz,
12
Bowaz shi ne mahaifin Obed kuma Obed shi ne mahaifin Yesse.
13
Yesse shi ne mahaifin. Eliyab ɗan farinsa, ɗansa na biyu shi ne Abinadab, na ukun Shimeya,
14
na huɗun Netanel, na biyar Raddai,
15
na shidan Ozem na bakwai kuma Dawuda.
16
’Yan’uwansu mata su ne Zeruhiya da Abigiyel. ’Ya’yan Zeruhiya maza guda uku su ne Abishai, Yowab da Asahel.
17
Abigiyel ita ce mahaifiyar Amasa, wanda mahaifinsa shi ne Yeter mutumin Ishmayel.
Settings