Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Ulam
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Ma’aka matar Makir ta haifi ɗa ta kuma ba shi suna Feresh. Sunan ɗan’uwansa Sheresh, ’ya’yan Feresh maza kuwa su ne Ulam da Rakem.
Ɗan Ulam shi ne, Bedan. Duka waɗannan zuriyar Gileyad ne. Gileyad ɗan Makir ne, Makir kuma ɗan Manasse.
’Ya’yan ɗan’uwansa Eshek su ne, Ulam ɗan farinsa, Yewush ɗansa na biyu da Elifelet na uku.
’Ya’yan Ulam maza jarumawa ne sosai waɗanda suke iya riƙe baka. Suna da ’ya’ya maza masu yawa da jikoki, 150 gaba ɗaya. Dukan waɗannan zuriyar Benyamin ne.