Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Torments

8 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa.

  2. Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’

  3. “Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba.

  4. Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’

  5. “Ya amsa ya ce, ‘To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina,

  6. gama ina da ’yan’uwana biyar maza. Bari yă ba su gargaɗi, don kada su ma su zo wurin nan mai azaba.’

  7. shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon.

  8. Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.”