Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Ten Commandments: Summed up Christ
Ayoyi game da Summed up Christ
Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya.
“Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?”
Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’
Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma.
Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’
Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.”