Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Moth

8 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. to, su wane ne mutane masu zama a gidan da aka yi da laka, waɗanda da ƙura aka yi harsashensu, waɗanda za a iya murƙushe su kamar asu!

  2. “Haka mutum yake lalacewa kamar ruɓaɓɓen abu, kamar rigar da asu ya cinye.

  3. Gidan da ya gina kamar gidan gizo-gizo, kamar bukkar mai tsaro.

  4. Ubangiji Mai Iko Duka ne zai taimake ni. Wane ne zai iya tabbatar da ni mai laifi? Duk za su koɗe kamar riga; asu za su cinye su.

  5. Gama asu za su cinye su kamar riga; tsutsotsi za su cinye su kamar ulu. Amma adalcina zai dawwama har abada, cetona har dukan zamanai.”

  6. Na zama kamar asu ga Efraim, kamar ruɓa ga mutanen Yahuda.

  7. “Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata.

  8. Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku.