Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Deluge: (Unexpectedness of,) of suddenness of Christ's coming

8 ayoyi · 27 fannoni

Ayoyi game da (Unexpectedness of,) of suddenness of Christ's coming

  1. “Babu wanda ya san wannan rana ko sa’a, ko mala’ikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.

  2. Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.

  3. Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi;

  4. ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.

  5. Mutane suna ci, suna sha, suna aurayya, ana kuma ba da su ga aure, har ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Sa’an nan ambaliyar ruwan ya sauka, ya hallaka su duka.

  6. “Haka ma aka yi a zamanin Lot. Mutane suna ci, suna sha, suna saya, suna sayarwa, suna shuki, suna kuma gine-gine.

  7. Amma a ranar da Lot ya bar Sodom, sai aka yi ruwan wuta da farar wuta daga sama, aka hallaka su duka.

  8. “Daidai haka zai zama, a ranar da Ɗan Mutum zai bayyana.