Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Deluge: Sent as a punishment for the extreme wickedness of man

6 ayoyi · 27 fannoni

Ayoyi game da Sent as a punishment for the extreme wickedness of man

  1. Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci.

  2. Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai.

  3. Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”

  4. Duniya dai ta lalace sosai a gaban Allah, ta kuma cika da tashin hankali.

  5. Allah ya ga yadda duniya ta lalace, gama dukan mutane a duniya sun lalatar da rayuwarsu.

  6. Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, “Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya.