Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Testament

7 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.

  2. Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa.

  3. Haka kuma, bayan abincin, ya ɗauki kwaf ruwan inabi ya ce, “Wannan kwaf ruwan inabi shi ne, na sabon alkawari cikin jinina, da aka zubar dominku.

  4. Haka kuma bayan cimar, ya ɗauki kwaf, yana cewa, “Wannan kwaf ne sabon alkawari a jinina; ku yi wannan, a duk sa’ad da kuke sha, don tunawa da ni.”

  5. Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta,

  6. domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai.

  7. Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini.