Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Straight

5 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Muryar wani tana kira cewa, “A cikin hamada ku shirya hanya saboda Ubangiji; ku miƙe manyan hanyoyi domin Allahnmu a cikin jeji.

  2. Za a cike kowane kwari, a baje kowane dutse da kowane tudu; za a mayar da karkatattun wurare su zama sumul, munanan wurare kuma su zama da kyau.

  3. Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa, “Ga murya mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”

  4. Ubangiji ya ce masa, “Je gidan Yahuda da yake a Miƙaƙƙen Titi ka yi tambaya ko akwai wani mutum daga Tarshish mai suna Shawulu, gama ga shi yana addu’a.

  5. “Ku shirya hanyoyi marasa gargaɗa saboda ƙafafunku,” don kada guragu su daɗa gurguntawa, sai dai su warke.