Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Spitting
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Da a ce mahaifinta ne ya tofa mata miyau a fuskarta, ashe, ba za tă ji kunya har kwana bakwai ba? A fitar da ita bayan sansani kwana bakwai; bayan haka za a iya dawo da ita.”
sai gwauruwan nan, matar ɗan’uwansa tă haura wurinsa a gaban dattawa, tă tuɓe takalminsa guda, ta tofa masa miyau a fuska, tă ce, “Haka za a yi ga mutumin da zai ƙi kafa gidan ɗan’uwansa.”
Suna ƙyamata suna guduna; suna tofa mini miyau a fuska.
Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi
Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai.
Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin.
Yesu ya kama hannun makahon ya kai shi bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun mutumin, ya kuma ɗibiya masa hannuwansa, sai ya tambaye shi ya ce, “Kana iya ganin wani abu?”