Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Spiritual Life

14 ayoyi · 29 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”

  2. Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!”

  3. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.

  4. Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu.

  5. Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’

  6. Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.”

  7. Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.”

  8. Sai Yahudawa suka fara gardama mai tsanani a junansu suna cewa, “Yaya wannan mutum zai ba mu naman jikinsa mu ci?”

  9. Sai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba.

  10. Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne.

  11. Amma in Kiristi yana a cikinku, jikinku matacce ne saboda zunubi, duk da haka ruhunku yana a raye saboda adalci.

  12. In kuwa Ruhu wannan da ya tā da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya tā da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku.

  13. Saboda haka ’yan’uwa, muna da hakki, amma ba na wanda za mu yi rayuwar mutuntaka da yake so ba.

  14. Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu.