Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sower: Figurative

7 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da Figurative

  1. Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki.

  2. Mugun mutum kan sami albashin ƙarya amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce.

  3. zai zama muku da albarka, ku da kuke shuki iri kusa da kowane rafi, kuna kuma barin lafiyayyiyar makiyaya domin shanu da jakunanku.

  4. “Gama sun shuka iska don haka za su girbe guguwa. Hatsin da yake tsaye ba shi da kai, ba zai yi tsaba ba. Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci.

  5. Ku shuka wa kanku adalci, ku girbe ’ya’yan jinƙai marar ƙarewa, ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba; gama lokaci ne na neman Ubangiji, sai ya zo ya zubo adalci a kanku.

  6. Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne.

  7. Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.