Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sisera

17 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Daga sama taurari suka yi faɗa, daga bakin tekuna suka yi yaƙi da Sisera.

  2. Kogin Kishon ya kwashe su, tsohon kogi, kogin Kishon. Ci gaba raina; ka ƙarfafa!

  3. Sa’an nan kofatan dawakai suka ƙwaƙula, suna sukuwa, haka dawakansa masu ƙarfi suke tafiya.

  4. Mala’ikan Ubangiji ya ce, ‘Ka la’anci Meroz.’ ‘Ka la’anci mutanensa sosai, domin ba su kawo wa Ubangiji taimako ba, su kawo wa Ubangiji taimako a kan masu ƙarfi ba.’

  5. “Mafi albarka a ciki mata ta zama Yayel matar Heber Bakene, mafi albarka na mata masu zama a alfarma.

  6. Ya nemi ruwa, ta kuwa ta ba shi madara; a ƙwaryar da ta dace da sarakuna ta kawo masa kindirmo.

  7. Hannunta ya ɗauki turken tenti, da hannunta na dama ta ɗauko guduma. Ta bugi Sisera, ta ragargaza kansa, ta ragargaza ta huda kunnensa.

  8. A ƙafafunta ya fāɗi, ya fāɗi; a can ya kwanta. A ƙafafunta ya fāɗi, ya fāɗi; a can ya fāɗi, matacce.

  9. “Ta taga mahaifiyar Sisera ta leƙa; a bayan madogarar ƙofa ta yi ta ihu, ‘Me ya sa keken yaƙinsa ta daɗe ba tă dawo ba? Me ya sa dawakan keken yaƙinsa ba su dawo da wuri ba?’

  10. Mafi hikima cikin ’yan matanta suka amsa mata, tabbatacce, ta ci gaba ta ce wa kanta,

  11. ‘Ba nema suke su raba ganima ba, yarinya guda ko biyu wa kowane mutum, riguna masu launi a matsayin ganima don Sisera, riguna masu ado, riguna masu ado sosai don wuyata, dukan wannan a matsayin ganima?’

  12. “Ta haka bari dukan abokan gābanka su hallaka, ya Ubangiji! Amma bari waɗanda suke ƙaunarka su zama kamar rana sa’ad da ta fito da ƙarfinta.” Sa’an nan ƙasar ta sami zaman lafiya shekara arba’in.

  13. Amma suka manta da Ubangiji Allahnsu, shi kuma ya bashe su a hannun Sisera shugaban rundunar Hazor da kuma hannun Filistiyawa da sarkin Mowab wanda suka yi yaƙi da su.

  14. Barkos, Sisera, Tema,

  15. da ta Barkos, da ta Sisera, da ta Tema,

  16. Ka yi musu abin da ka yi wa Midiyan, yadda ka yi wa Sisera da Yabin a kogin Kishon,

  17. Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu.