Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Simplicity: In preaching the gospel

5 ayoyi · 20 fannoni

Ayoyi game da In preaching the gospel

  1. Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba.

  2. A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yă danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu.

  3. Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu.

  4. Ba ma neman yabo daga wurin mutane, ko a gare ku, ko ga waɗansu. A matsayinmu na manzannin Kiristi da mun so, da mun nawaita muku,

  5. amma muka kasance masu sauƙinkai a cikinku, kamar yadda mahaifiya take lura da ƙananan ’ya’yanta.