Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rephidim

5 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Dukan taron Isra’ilawa suka kama tafiya daga Hamadar Sin, suka yi ta tafiya suna sauka a wurare dabam-dabam bisa ga umarnin Ubangiji. A ƙarshe suka sauka a Refidim, suka zauna a can, amma ba ruwan da jama’a za su sha.

  2. Amalekawa suka zo, suka yaƙi Isra’ilawa a Refidim.

  3. Bayan da suka tashi daga Refidim, suka shiga Hamadar Sinai, sai Isra’ilawa suka yi sansani a gaban dutsen.

  4. Suka tashi daga Alush, suka yi sansani a Refidim, inda babu ruwan da mutane za su sha.

  5. Suka tashi daga Refidim, suka yi sansani a Hamadan Sinai.