Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Railing: Forbidden

5 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Forbidden

  1. Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum.

  2. yana cike da girman kai bai kuma san kome ba. Yana da mugun halin son gardama da muhawwara game da kalmomin da suke kawo kishi, rikici, maganar ƙeta, da mugayen zace-zace

  3. Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka.

  4. duk da haka ko mala’iku ma da suka fi su ƙarfi suka kuma fi su iko, ba sa kawo irin wannan zargi na ɓata suna game da waɗannan talikai a gaban Ubangiji.

  5. Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!”