Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Proselyte

6 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai.

  2. amma rana ta bakwai, Asabbaci ne ga Ubangiji Allahnka. A kanta ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawanka, ko baiwarka, ko saniyarka, ko jakinka, ko wani daga dabbobinka, ko baƙo a ƙofofinka, don bayinka maza da mata su ma su huta, kamar ka.

  3. “Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashe, ku ƙetare teku don ku sami mai tuba ɗaya, sa’ad da ya tuba kuwa, sai ku mai da shi ɗan wuta fiye da ku, har sau biyu.

  4. Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma

  5. Wannan shawarar kuwa ta gamshi dukan ƙungiyar. Sai suka zaɓi Istifanus, mutumin da yake cike da bangaskiya da kuma Ruhu Mai Tsarki; da Filibus, Burokorus, Nikano, Timon, Farmenas, da Nikolas daga Antiyok, wanda ya tuba zuwa Yahudanci.

  6. Da aka sallami jama’a, Yahudawa da yawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci masu ibada suka bi Bulus da Barnabas, waɗanda suka yi magana musu suka kuma ƙarfafa su su ci gaba a cikin alherin Allah.