Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Priest

14 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. To, fa, akwai wani firist na Midiyan, yana da ’ya’ya mata bakwai, suka zo su shayar da dabbobin mahaifinsu.

  2. za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.”

  3. Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa.

  4. Sun auro wa kansu da ’ya’yansu ’yan mata mutanen nan, ta haka aka kwaɓa zuriyar da aka tsarkake da ta mutanen nan da suke tare da su. Shugabanni da manyan ma’aikata su ne a gaba-gaba a aikata wannan abin kunya.”

  5. Sai Ezra ya tashi ya sa firistoci da suke shugabanni, da Lawiyawa, da dukan mutanen Isra’ila su rantse, cewa za su yi abin da aka ce. Sai suka yi rantsuwar.

  6. A cikin zuriyar firistoci, ga waɗanda suka auri mata baƙi. Daga zuriyar Yeshuwa ɗan Yozadak da ’yan’uwansa, akwai Ma’asehiya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya.

  7. (Su ne suka miƙa hannuwansu suka nuna sun yarda su kori matansu baƙi, kowannensu kuma ya ba da rago daga cikin garkensa don a miƙa hadaya don zunubi.)

  8. “Sauran mutane, wato, firistoci, Lawiyawa, matsaran ƙofofi, mawaƙa, ma’aikatan haikali da dukan waɗanda suka ware kansu daga maƙwabta saboda Dokar Allah, tare da matansu da dukan ’ya’yansu maza da mata waɗanda za su iya fahimta,

  9. Za a kuma kira ku firistocin Ubangiji, za a kira ku masu hidimar Allahnmu. Za ku ci wadatar waɗansu al’ummai, kuma a cikin dukiyarsu za ku yi taƙama.

  10. Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu.

  11. Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.

  12. ya kuma mai da mu masarauta da firistoci don mu yi wa Allahnsa da Ubansa hidima, a gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin! Amin.

  13. Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima, kuma za su yi mulki a duniya.”

  14. Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.