Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Pedaiah

8 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Zebuda ’yar Fedahiya, mutuniyar Ruma.

  2. Malkiram, Fedahiya, Shenazzar, Yekamiya, Hoshama da Nedabiya.

  3. ’Ya’yan Fedahiya su ne, Zerubbabel da Shimeyi. ’Ya’yan Zerubbabel maza su ne, Meshullam da Hananiya. Shelomit ce ’yar’uwarsu.

  4. bisa mutanen Efraim shi ne, Hosheya ɗan Azaziya; bisa rabin kabilar Manasse shi ne, Yowel ɗan Fedahiya;

  5. sai Falal ɗan Uzai ya yi aiki ɗaura da kusurwa da kuma doguwar hasumiya daga fadar da take bisa kusa da shirayin masu tsaro. Biye da shi, Fedahiya ɗan Farosh

  6. Ezra malamin Doka ya tsaya a kan dakalin itacen da aka yi saboda wannan hidima. Kusa da shi a damansa, Mattitiya, Shema, Anahiya, Uriya, Hilkiya da Ma’asehiya suka tsaya; a hagunsa kuma Fedahiya, Mishayel, Malkiya, Hashum, Hashbaddana, Zakariya da Meshullam suka tsaya.

  7. Daga zuriyar Benyamin akwai, Sallu ɗan Meshullam, ɗan Yowed, ɗan Fedahiya, ɗan Kolahiya, ɗan Ma’asehiya, ɗan Itiyel, ɗan Yeshahiya,

  8. Na sa Shelemiya firist, Zadok marubuci, da wani Balawe mai suna Fedahiya su lura da ɗakunan ajiya na kuma sa Hanan ɗan Zakkur, ɗan Mattaniya ya zama mataimakinsu, domin an ɗauka waɗannan mutane amintattu ne. Aka ba su hakkin raban kayayyaki wa ’yan’uwansu.