Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Nile

11 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ubangiji zai busar da bakin tekun Masar; da iska mai zafi zai share hannunsa a bisa Kogin Yuferites Zai rarraba shi yă zama ƙanana rafuffuka bakwai saboda mutane su iya hayewa da ƙafa.

  2. Ruwayen kogi za su ƙafe, bakin kogi zai shanye yă kuma bushe.

  3. Wuriyoyi za su yi wari; rafuffukan Masar za su yi ta raguwa har su ƙafe. Iwa da jema za su bushe,

  4. haka ma tsire-tsire kusa da Nilu, a bakin kogi. Kowane abin da aka shuka a gefen Nilu zai bushe, iska ta kwashe su ƙaf.

  5. Masu kamun kifi za su yi nishi su kuma yi makoki, dukan waɗanda suke jefan ƙugiyoyi a Nilu; waɗanda suke jefan abin kamun kifi a ruwa abin kamun kifin za su zama marasa amfani.

  6. Waɗanda suke aiki da kaɗin auduga za su karai, masu yin lilin mai kyau za su fid da zuciya.

  7. Masu aikin tufafi ransu zai ɓace, kuma dukan masu samun albashi za su damu.

  8. A manyan ruwaye hatsin Shihor suka iso; girbin Nilu ne kuɗin shiga na Taya ta kuma zama kasuwar al’ummai.

  9. To, me ya sa za ka Masar don shan ruwa daga Shihor? Kuma me ya sa za ka Assuriya don shan ruwa daga Kogi?

  10. Amma zan sa ƙugiyoyi a muƙamuƙanka in sa kifin rafuffukanka su manne wa kamɓorinka. Zan jawo ka daga cikin tsakiyar rafuffukanka, da dukan kifayen rafuffukanka, waɗanda suka manne a ƙamborinka,

  11. “Shin, ƙasar ba za tă yi rawan jiki saboda wannan ba, kuma duk masu zama a cikinta ba za su yi makoki ba? Ƙasar duka za tă hau ta sauka kamar Nilu; za a dama ta sa’an nan ta nutse kamar kogin Masar.