Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Name: Symbolic

5 ayoyi · 2 fannoni

Ayoyi game da Symbolic

  1. Saboda haka sai ya auri Gomer ’yar Dibilayim, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa namiji.

  2. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba shi suna Yezireyel, domin ba da daɗewa ba zan hukunta gidan Yehu saboda kisan da aka yi a Yezireyel, zan kuma kawo ƙarshen mulkin Isra’ila.

  3. Gomer ta sāke ɗauki ciki ta kuma haifi ’ya mace. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba ta suna, Lo-Ruhama, gama ba zan ƙara nuna wa gidan Isra’ila ƙauna ba, har da zan gafarta musu.

  4. Sai Ubangiji ya ce, “Ka ba shi suna Lo-Ammi, gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.

  5. “Ka ce da ’yan’uwanka maza, ‘Mutanena,’ ka kuma ce da ’yan’uwanka mata, ‘Ƙaunatacciyata.’