Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Naashon

8 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Haruna ya auri Elisheba, ’yar Amminadab, ’yar’uwar Nashon, sai ta haifa masa Nadab da Abihu, Eleyazar da Itamar.

  2. daga kabilar Yahuda, Nashon ɗan Amminadab;

  3. Kabilar Yahuda za su yi sansani bisa ga ƙa’idarsu a gabas, wajen fitowar rana. Shugaban mutanen Yahuda kuwa shi ne Nashon ɗan Amminadab.

  4. Wanda ya kawo hadayarsa a rana ta farko shi ne Nashon ɗan Amminadab, shugaban mutanen Yahuda.

  5. da shanu biyu, raguna biyar, bunsurai biyar da kuma ’yan raguna biyar dukansu bana ɗaya-ɗaya, a miƙa su hadaya ta salama. Wannan ita ce hadayar Nashon ɗan Amminadab.

  6. Ɓangarorin sansanin Yahuda suka fara tashi, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Nashon ɗan Amminadab ne shugaba.

  7. Ram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon,

  8. ɗan Yesse, ɗan Obed, ɗan Bowaz, ɗan Salmon, ɗan Nashon,