Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Myrrh: Traffic in
Ayoyi game da Traffic in
Da suka zauna don cin abinci, sai suka tā da idanu, suka ga ayarin mutanen Ishmayel suna zuwa daga Gileyad. An yi wa raƙumansu labtu da kayan yaji da na ƙanshi, suna kan hanyarsu za su Masar.
Sa’an nan mahaifinsu Isra’ila ya ce musu, “In dole ne a yi haka, to, sai ku yi. Ku sa waɗansu amfani mafi kyau na ƙasar a buhunanku, ku ɗauka zuwa wurin mutumin a matsayin kyauta, da ɗan man ƙanshi na shafawa, da kuma ’yar zuma, da kayan yaji, da ƙaro, da tsabar citta da kuma almon.