Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Miriam: Watches over Moses when he is in the ark

5 ayoyi · 4 fannoni

Ayoyi game da Watches over Moses when he is in the ark

  1. ’Yar’uwarsa ta tsaya da ɗan rata tana lura da abin da zai faru da shi.

  2. Sai ’yar Fir’auna ta gangara zuwa kogi domin tă yi wanka, bayinta kuwa suna tafiya a bakin kogi. Sai ta ga kwandon a ciyawa, ta aiki ɗaya daga cikin masu hidimarta tă ɗauko mata.

  3. Da ta buɗe kwandon, sai ta ga yaro yana kuka, ta kuwa ji tausayinsa. Ta ce, “Wannan ɗaya daga cikin jariran Ibraniyawa ne.”

  4. Sai ’yar’uwarsa ta tambayi ’yar Fir’auna, ta ce, “In tafi in samo ɗaya daga cikin matan Ibraniyawa tă yi miki renon yaron?”

  5. Sai ta amsa ta ce, “I, tafi.” Sai yarinyar ta tafi ta kawo mahaifiyar yaron.