Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Malefactor

15 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. An gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa.

  2. Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai,

  3. suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”

  4. Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa,

  5. “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi.

  6. Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ”

  7. Haka ma, ’yan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi.

  8. Tare da shi akwai mutum biyu masu laifi, da aka tafi da su don a gicciye.

  9. Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa.

  10. Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.

  11. Mutanen suka tsaya suna kallo. Har masu mulki ma suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe.”

  12. Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami.

  13. Suka ce, “In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana.”

  14. Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce, Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.

  15. Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye a wurin ya zazzage shi ya ce, “Shin, ba kai ne Kiristi ba? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!”