Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Machpelah: The burial place of Sarah, Abraham, Isaac, Rebekah, Leah, and Jacob.
Ayoyi game da The burial place of Sarah, Abraham, Isaac, Rebekah, Leah, and Jacob.
Ta haka filin Efron a Makfela kusa da Mamre, wato, filin da kogon a cikinsa, da kuma dukan itatuwan da suke cikin iyakoki filin, aka
ba wa Ibrahim a matsayin mallakarsa a gaban dukan Hittiyawa waɗanda suka zo ƙofar birnin.
Bayan wannan Ibrahim ya binne matarsa Saratu a kogon a filin Makfela kusa da Mamre (wanda yake a Hebron) a ƙasar Kan’ana.
Da filin da kuma kogon da yake cikinsa, Hittiyawa suka tabbatar wa Ibrahim a matsayin makabarta.
kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti.
A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu.