Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Lust: Evil desire

17 ayoyi · 1 fanni

Ayoyi game da Evil desire

  1. “In sha’awar mace ya shiga mini zuciya, ko kuma na laɓe a ƙofar maƙwabcina,

  2. sai matata ta niƙa hatsin wani kuma waɗansu maza su kwana da ita.

  3. Gama wannan zai zama abin kunya, zunubin da za a yi shari’a a kai.

  4. Wuta ce take ƙuna har ta hallakar; za tă cinye saiwar abin da na shuka ƙurmus.

  5. suna kiyaye ka daga mace marar ɗa’a daga sulɓin harshen mace marar aminci.

  6. Kada ka yi sha’awarta a cikin zuciyarka kada ka bar ta tă ɗauki hankalinka da idanunta.

  7. To, waɗannan abubuwa misalai ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi.

  8. Kada ku zama masu bautar gumaka, yadda waɗansunsu suka zama; kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mutanen suka zauna don su ci su kuma sha, suka kuma tashi suka shiga rawa ta rashin kunya.”

  9. Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji.

  10. Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi.

  11. amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi.

  12. Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa.

  13. Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne?

  14. Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba.

  15. Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku.

  16. Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya.

  17. Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.