Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Lamp

21 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. “Ka yi wurin ajiye fitilar da zinariya zalla, ka kuma yi gindinsa tare da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya; kwafunansa da suka yi kamar furanni, tohonsa da furanninsa su yi yadda za su zama ɗaya da shi.

  2. Wurin ajiye fitilar yă kasance da rassa shida, rassan nan za su miƙe daga kowane gefe na wurin ajiye fitilan, uku a gefe guda, uku kuma a ɗaya gefen.

  3. Kwafuna uku masu siffar furanni almon, da toho, da kuma furannin za su kasance a rashe guda, uku a kan rashe na biye, haka kuma a kan saura rassan shida da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan.

  4. A bisa wurin ajiye fitilan kuwa za a kasance da kwafuna huɗu masu siffar furannin almon, da toho, da furanni.

  5. Toho ɗaya zai kasance a ƙarƙashin rassa biyu na farkon da suka miƙe daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku a ƙarƙashin rassa na uku, rassa shida ke nan duka.

  6. Tohon da kuma rassan za su kasance ɗaya da wurin ajiye fitilan da aka yi da ƙerarriyar zinariya.

  7. “Sa’an nan ka yi fitilu bakwai, ka sa su a bisa wurin ajiye fitilan ta yadda za su haskaka wajen da suka fuskanta.

  8. Za a yi lagwaninsa da manyan farantansa da ƙerarriyar zinariya.

  9. Da zinariya zalla na talenti ɗaya za ka yi wurin ajiye fitilan da waɗannan abubuwa duka.

  10. Sai ka lura ka yi su daidai bisa ga fasalin da aka nuna maka a kan dutse.

  11. “Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai, tatacce daga zaitun domin fitilu, saboda fitilun su yi ta ci a koyaushe.

  12. A cikin Tentin Sujada, a waje da labulen da yake a gaban Akwatin Alkawari, Haruna da ’ya’yansa za su sa fitilu su yi ta ci a gaban Ubangiji, daga yamma har safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a cikin Isra’ila har tsararraki masu zuwa.

  13. Suka yi wurin ajiye fitila da zinariya zalla, suka yi gindinsa da kuma gorar jikinsa, da ƙerarriyar zinariya. Kwaf wurin ajiye fitila da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da wurin ajiye fitilan.

  14. Akwai rassa guda shida da suka miƙe daga gefe wurin ajiyar fitilar, uku a wannan gefe, uku kuma a wancan.

  15. A reshe guda na wurin ajiye fitilan, akwai kwaf uku masu kama da tohon almon, akwai kuma uku a reshe na biye, haka kuma suke a dukan rassa shida da suke daga wurin ajiye fitilan.

  16. A bisa wurin ajiye fitilan kuma akwai kwaf huɗu da aka yi su kamar furannin almon da toho da kuma mahaɗai.

  17. Toho ɗaya yana a ƙarƙashin rassa biyu waɗanda suke daga wurin ajiye fitilan, toho na biyu yana a ƙarƙashin rassa biyu na biye, toho na uku kuma yana a ƙarƙashin rassa biyu na uku, duka-duka rassa shida ne.

  18. An ƙera mahaɗai da rassa wurin ajiye fitila a haɗe. Da ƙerarriyar zinariya aka yi wurin ajiye fitilar da dukan komensa a haɗe.

  19. “Ka umarci Isra’ilawa su kawo tsabtataccen mai na zaitun da aka matse, don ƙuna fitilun yadda harshen wutar ba zai taɓa mutuwa ba.

  20. Za a ajiye su waje da labulen Wuri Mafi Tsarki a Tentin Sujada, Haruna zai riƙa kula da fitilun a gaban Ubangiji, daga yamma zuwa safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa tsararraki masu zuwa.

  21. Dole a ci gaba da shirya fitilu a kan wurin ajiye fitila na zinariya, a gaban Ubangiji.