Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Jephthah: Made captain of the host

7 ayoyi · 12 fannoni

Ayoyi game da Made captain of the host

  1. dattawan Gileyad suka je suka nemo Yefta daga ƙasar Tob.

  2. Suka ce masa, “Ka zo ka zama mana shugaba, don mu yaƙi Ammonawa.”

  3. Yefta ya ce musu, “Ba kun ƙi ni kuka kuma kore ni daga gidan mahaifina ba? Me ya sa kuke zuwa wurina yanzu sa’ad da kuke cikin wahala?”

  4. Mutanen Gileyad suka ce masa, “Duk da haka, muna juyo wajenka yanzu, ka zo tare da mu mu yaƙi Ammonawa, za ka kuma zama shugaban duk wanda yake zama a Gileyad.”

  5. Yefta ya ce, “A ce kun dawo da ni in yaƙi Ammonawa, Ubangiji kuwa ya ba da su a hannuna, zan zama shugabanku?”

  6. Dattawan Gileyad suka ce, “Ubangiji ne shaidanmu; za mu yi duk abin da ka ce.”

  7. Saboda haka Yefta ya tafi tare da dattawan Gileyad, mutanen kuwa suka naɗa shi shugabansu da kuma sarkinsu. Ya kuwa maimaita dukan maganarsa a gaban Ubangiji a Mizfa.