Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Good and Evil: Conflict between

9 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da Conflict between

  1. Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan.

  2. Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki.

  3. “Ga shi, ina zuwa kamar ɓarawo! Mai albarka ne wanda yake zama a faɗake yana kuma saye da tufafinsa, don kada yă yi tafiya tsirara a kuma kunyata shi.”

  4. Sa’an nan aka tattara sarakuna zuwa wurin da a Ibraniyanci ake kira Armageddon.

  5. Mala’ika na bakwai ya juye kwanonsa cikin iska, daga haikalin kuwa sai aka ji wata babbar murya daga kursiyin, tana cewa, “An gama!”

  6. Sai ga walƙiya, ƙararraki, tsawa da kuma matsananciyar girgizar ƙasa. Ba a taɓa yin irin wannan girgizar ƙasar ba, tun kasancewar mutum a duniya, girgizar ƙasar kuwa gawurtacciya ce.

  7. Babban birnin ya rabu kashi uku, biranen al’ummai kuma suka rurrushe. Allah ya tuna da Babilon Mai Girma ya kuma ba ta kwaf cike da ruwan inabin fushinsa.

  8. Kowane tsibiri ya gudu ba a kuwa ƙara ganin duwatsu ba.

  9. Daga sararin sama manyan ƙanƙara masu nauyin gaske suka fāɗo a kan mutane. Suka kuma la’anci Allah saboda annobar ƙanƙarar, domin annobar ta yi muni ƙwarai.